Sabunta ƙira ga gwamnatin jihar Katsina cewa ta shirya zaman muƙabala tsakanin Malaman jihar Katsina da masussuka mai zagin hadithan Annabi tare da ƙaryata su da yin musu isgili a gaban Duniya.
Lalle abu ne mai matuƙar kyau gwamnatin jihar Katsina ta yi kamar yadda gwamnatin jihar Kano ta taɓa yi na wajabta muƙabala tsakanin malaman jihar Kano da Abdul Jabbar Nasiru Kabara mai zagin wasu daga cikin Hadithai, mai jingina wa Annabi mai tsira da amincin Allah a bin da bai jingina wa kansa ba.