1. Yin Sadlu cikin salla sabanin sunnar Annabi Muhammad ne mai tsira da amincin Allah; domin asalin al’amari game da Ibadah shi ne hana yin ibadar har sai nassi ko mai tsayuwa matsayin nassi ya halatta yin ta tukun.
2. Abu ne sananne cewa: Dukkan wani mai yin Sadlu yana yin Sadlun ne a matsayin Ibadah alhali kuwa babu nassi daga Allah ko daga ManzonSa da ya ce a yi Sadlu cikin Salla, kai hasali ma Nassin da ya zo daga Manzon Allah shi ne: Umurni da yin kishiyar Sadlu wato Kabdhu, ke nan yin Sadlu sabanin Sunnar Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah ne.
3. Maluma da dama ne suka bayyana wa Duniya cewa yin Sadlu sabanin Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne, daga cikin wadannan Malamai akwai Sheikh Abdul Aziz Bin Baz a inda ya ce cikin Majmuu’ul Fataawaa nasa 11/144:-
((اما ارسال اليدين في الصلاة فمكروه لا ينبغي فعله لكونه خلاف السنة؛ وقد ثبت في صحيح البخاري عن ابي حازم عن سهل بن سعد رضي الله عنه قال: كانوا يومرون ان يضع الرجل يده اليمنى على ذراعه اليسرى في الصلاة)).
Ma’ana: ((Amma sake hannaye biyu cikin salla makruhi ne, yin shi ba ya dacewa saboda kasancewarsa sabanin Sunnah; domin ya tabbata cikin Sahihiul Bukhariy daga Abu Haazim daga Sahl Bin Sa’ad Allah Ya kara masa yarda ya ce: Sun kasance ana umurtan su da cewa mutum ya dora hannunsa na dama a kan ziraa’in hagunsa cikin Sallah)).
4. Allah muke rokon Ya taimake mu Ya cusa mana son bin Sunnah cikin aqidarmu da ibadarmu da kuma mu’amalarmu. Ameen.
After study a few of the blog posts on your website now, and I truly like your way of blogging. I bookmarked it to my bookmark website list and will be checking back soon. Pls check out my web site as well and let me know what you think.
Your article helped me a lot, is there any more related content? Thanks!
Can you be more specific about the content of your article? After reading it, I still have some doubts. Hope you can help me. https://accounts.binance.com/id/register?ref=GJY4VW8W