1. Cikin Sahabbai Mata akwai wadanda Shari’ar Musulunci ta ba su izinin halartan fagen daga domin hidimar abinci da abin sha, da kuma hidimar jinya tare da taimaka wa mayakan da aka yi musu rauni, wadannan su ne suka fi yawa.
2. Sannan kuma akwai wadanda Shari’ar Musulunci ta ba su damar daukar makami da yin yakin buga in buga da kafurai makiya Allah da ManzonSa, wadannan su ne kadan.
3. Daga cikin matan da suka yi yaki a fagen daga a zamanin Manzon Allah da Abubakar Siddeeq akwai Sahabiya Ummu Umarah Nusaibah Bint Ka’ab, wacce ta rasu a shekarar hijira ta goma sha uku.
4. Sahabiya Nusaibah ta yi yaki a ranar yakin Uhd, ta kuma nuna bajinta kwarai gurin kare Manzon Allah mai tsira da aminci a inda har aka yi mata rauni 13 tsakanin sarar takobi da sukar mashi. Haka nan Nusaibah ta yi yaki a ranar yakin Hunain, kuma ta nuna bajinta matuka. Haka nan ta yi yaki a lokacin yake yake ridda, a karkashin Sahabi Khalid Bin Waleed.
5. A ranar da aka yi yakin karshe da rundunar makiyin Allah Musailamah ne riddaddu suka yanke mata hannu a fagen daga wanda hakan ya kasance ajalinta bayan jinyar wani lokaci.
6. Ya Allah Ka kara yarda da Sahabbai maza da mata. Ameen.
Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me? https://www.binance.com/ar-BH/register?ref=V2H9AFPY
Your article helped me a lot, is there any more related content? Thanks!