Farko dai yana da kyau a san cewa shi yin sallar Tahajjud a cikin jama’a a cikin goman karshe na Ramadan da al’ummar Musulmi ke yi abu ne da ya dace da ingantacciyar Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah; saboda hadithai sun inganta a kan cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya yi wa al’ummar Musulmi maza da mata limancin wannan salla a cikin wasu daga cikin wadannan kwanaki da muka ambata.
Abu na biyu shi ne yana da kyau a san cewa shi limamin jama’a yana bayyanar da karatunsa ne cikin irin wadannan salloli na dare; duk kuwa inda bayyanar da karatun sallar liman ya shar’anta ko ya halatta to ya halatta shi limamin ya yi wannan karatu nasa sifika kuma ta dauka, babu sabanin mujtahidai cikin wannan lamarin a iya sanina; kamar dai yadda al’amarin yake a cikin sauran salloli da limamai ke jagoranta, watau sallolin farilla guda biyar, da sallolin Idi guda biyu, da makamantansu.
Allah muke rokon Ya karbi ibadodinmu, Ya kuma taimake mu har kullum. Ameen.