1. Sayyidina Aliyyu Allah Ya kara masa yarda ba ma’asumi ba ne shi kamar yadda Rafidhawa suke ikirari, a’a, shi Mutum ne Sahabi Ahlul Baiti, yana iya yin kure, kuma yana iya yin daidai kamar dai yadda sauran Sahabbai ‘yan’uwansa suke: Muhajirai da Ansar, Ahlul Baiti daga cikinsu da wadanda suke ba Ahlul Baiti ba, wannan shi ne matsayinsa a Shari’ar Musulunci babu ragi babu kari.

2. Wasu suna yin kure; domin neman kara daukaka darajar shi Sayyidina Aliyyu har ka ga suna ta rubuta wa Duniya Hadithai masu rauni game da shi, duk da kuwa cewa akwai hadithai ingantattu bilaa adadin da suke bayyana darajarsa a idanun Shari’ar Musulunci.

3. Akwai wani dazu da ya yi posting wani hadithi mai rauni da hakim ya ruwaito, ga hafithin nan:
‎عَنْ حَیَّانَ الْأَسَدِیِّ، سَمِعْتُ عَلِیًّا یَقُولُ: قَالَ لِی رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَیْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الْأُمَّةَ سَتَغْدِرُ بِکَ بَعْدِی، وَأَنْتَ تَعِیشُ عَلَى مِلَّتِی، وَتُقْتَلُ عَلَى سُنَّتِی، مَنْ أَحَبَّکَ أَحَبَّنِی، وَمَنْ أَبْغَضَکَ أَبْغَضَنِی، وَإِنَّ هَذِهِ سَتُخَضَّبُ مِنْ هَذَا» – یَعْنِی لِحْیَتَهُ مِنْ رَأْسِهِ
Imam Albaniy ya ce a cikin littafinsa:
‎سلسلة الاحاديث  الضعيفة والموضوعة وأثرها السيئ في الأمة
Mujalladi na 10 shafi na 552 za ka ga Albaniy ya rubuta kamar haka:
‎((٤٩٠٥ “ان الأمة ستغادر بك بعدي” ضعيف . اخرجه الحاكم ٣/ ١٤٠ والخطيب في التاريخ ١١/ ٢١٦ وابن عساكر ١٢/ ١٧٨/٢.

4. Sannan da za a kaddara ingancin wannan Hadithin toh da sam babu wani abu a ckinsa da yake nuna cewa Sayyidina Aliyyu ma’asumi ne shi, ko kuwa shi ne Annabi mai tsira da amincin Allah ya nada Khalifan farko bayan mutuwarsa.

5. Saboda haka ni ina gani domin a kare mutuncin shi Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib Allah ya kara masa yarda daga sharrin ‘yan bidi’ar da suke daukar shi ma’asumin da baya yin kure, ba ya kuma sabon Allah mudlakan; yana da kyau daliban ilmin Shari’ar Musulunci su rika kawo kurakurensa wadanda suke nuna mutuntakarsa da kasancewarsa kamar sauran Sahabbai cikin Muhajirai da kuma Ansar, wadanda dukkansu suna iya yin kure kuma suna iya yin daidai.

6. Sayyidina Aliyyu Bin Talib a matsayinsa na dan adam yana da kurakurai da yawa wadanda suka tabbata cikin ingantattun Hadithai: hadithan Ahlus Sunnah da kuma hadithan Shi’ah Rafidha, ga misali daya na kuren da ya yi. Wannan kuren kuwa shi ne: a lokacin da ya nemi yin jayayya da Manzon Allah mai tsira da amincin Allah a lokacin da ya tambaye shi cewa: Me ya sa ba za ku yi sallar dare ba? maimakon ya ce wa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ji nasiharsa, kuma zai gyara, a’a, sai ya koma yin jayayya yana kafa wa Manzon Allah mai tsira da amincin Allah hujja da kaddara kauniyyah, wanda yin hakan a asali ba dabi’ar Muminai ba ce, a’a kafurai ne aka sani da yin hakan; Allah Madaukakin Sarki Ya ce cikin Suratu Yaseen ayah ta 47:-
‎((وإذا قيل لهم أنفقوا مما رزقكم الله قال الذين كفروا للذين ءامنوا ونطعم من لو يشاء الله أطعمه؟ إن أنتم إلا في ضلال مبين)).
Tarjama: ((Idan aka ce da su ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku sai wadannan da suka kafirta su gaya wa wadanda suka yi imani: Yanzu za mu ciyar da wanda in da Allah Ya ga dama Zai ciyar da shi? Ku dai ba ku kasance ba sai cikin bata bayyananna)).

7. Ga kissar abin da ya faru kamar yadda Imamul Bukhariy ya ruwaito cikin hadithi na 1,127, da Muslim na 775, da Nasaa’iy na 1,313, da Ahmad na 571, Ibnu Khuzaimah na 1,140, da Ibnu Hibban na 2,566, da Bazzar na 503. Ga nassin Hadithin:-
‎((عن علي بن ابي طالب رضي الله عنه قال: ان رسول الله صلى الله عليه وسلم طرقه وفاطمة عليها السلام ليلة فقال لهم: ألا تصلون؟ فقال علي: فقلت: يا رسول الله إنما أنفسنا بيد الله فإذا شاء أن يبعثنا بعثنا. فانصرف رسول الله صلى الله عليه وسلم حين قال له ذلك، ولم يرجع إليه شيئا، ثم سمعه وهو مدبر يضرب فخذه وهو يقول: وكان الإنسان أكثر شيء جدلا)).
Tarjama: ((An karbo daga Aliyyu Bin Abi Talib Allah Ya kara yarda da shi, ya ce: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya kwankwasa masa kofa cikin dare shi da Nana Fadimah alaihas salam, sannan ya ce da su: Ba za ku yi salla ba? Sai Aliyyu ya ce: Sai na ce: Ya Manzon Allah ai rayukanmu a hannun Allah suke, in Ya ga damar Ya tashe mu sai Ya tashe mu! A lokacin da ya fadi haka sai Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya juya abin shi, bai mayar masa da martanin kome ba. Daga sai ya ji shi a lokacin da ya ba da baya yana buga cinyarsa yana cewa: Mutum ya kasance mafi dukkan wani abu jayayya))!!
Wannan Hadithin su ma Shi’ah Rafidha sun ruwaito shi cikin Buhaarul Anwar na Majlisiy 40/160.

8. A inda za a gane kuren Sayyidina Aliyyu Bin Abi Talib a cikin Kissar shi ne irin yadda Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya karanta wani mangare na ayoyin da aka saukar a kan kafurai wadanda suke yin jayayya da shi a kan karya da son zuciya. Ga ayoyin nan a cikin Suratul Kahf: 54-56:-
‎((ولقد صرفنا في هذا القرآن للناس من كل مثل وكان الإنسان أكثر شيء جدلا. وما منع الناس أن يؤمنوا اذ جاء هم الهدى وبستغفروا ربهم إلا أن تاتيهم سنة الأولين او يأتيهم العذاب قبلا. وما نرسل المرسلين إلا مبشرين ومنذرين ويجادل الذين كفروا بالباطل ليدحضوا به الحق واتخذوا ءاياتي وما أنذروا هزوا)).

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *