
1. Muna bayar da shawara ga manƴan sojojinmu musulmi; sawaa’un tsoffin shugabannin ƙasa ne ko kuwa tsoffin gwamnoni ne, da ma waɗanda suke a kan muƙamansu a yanzu, da kuma manƴa manƴan generals ɗinmu da cewa ya kamata su riƙa yin wasiyyar cewa: a riƙa gudanar da jana’izarsu in rai ya yi halinsa a bisa tsantsar tsarin Musulunci kaɗai, ba tare da an garwaya shi da abin da ake ƙira da suna: Military Protocol, ko Military Decrees ba, a inda za a sanya makarar mamaci a tsakanin sojoji suna tafiya irin ta fareti, sashinsu na riƙe da furanni da lambobin yabo na shi mamacin, da abin da ya yi kama da haka, sannan wasu sojojin kuma suna ta kaɗe kaɗe da bushe bushe!
2. Tabbas irin waɗannan tsare tsare, da irin waɗannan bukukuwa sam sam ba za su dace da musulmi mai fiskantar shiga ƙabari ba, sam sam ba za su dace da musulmi mai fiskantar amsa tambayoyin manzannin Ubanginjnsa a cikin ƙabari ba
Masha-Allah, very informative, Allah Ya Saka da Alkhairi, Allah Ya karawa rayuwa Albarka.