SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA ƘASA JIBWIS NIGERIA YA ISA GARIN KATSINA DOMIN GABATAR DA WA’AZIN ƘASA

Isowar Dr. Jalo Gidan Sheikh Yakubu Musa

Shugaban Majalisar Malamai na Ƙasa Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo ya sauka a garin Katsina da misalin ƙarfe 07:00pm na yamma a yau Juma’a 20/10/2023 domin shirye shiryen gabatar da Wa’azi na Ƙasa da Ƙungiyar zata gabatar a ranakun Asabar da Lahadi 20-21/10/2023 In shaa Allah.

Shugaban Majalisar Malaman ya samu tarba na musamman daga Shugaban Ƙungiyar na Ƙasa Sheikh (DR) Abdullahi Bala Lau tare da Sakataren sa Sheikh Kabiru Haruna Gombe da Directorn Agaji na Ƙasa Mustapha Imam Sitti tare da Masauƙin Ɓaki Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus Sunnah da sauran Shugabannin Ƙungiyar a mataki na ƙasa.

Muna fata Allah Ta’aa’laa yasa ayi wannan wa’azi lafiya a tashi lafiya ya kuma amfanar da Al’umma da kuma ƙasa baki ɗaya fa’ida da kuma tasirin wannan Wa’azi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *