1. Masu addinin ƙalaƙato/tatsine/Ƙur’ani zalla da suke aske gemunsu sun saɓa wa Alƙur’ani mai girma, sun saɓa wa shiriyar Annabawa da Alƙur’ani ya bayar da umurnin a bi.
2. A cikin Alƙur’ani mai girma, a suratu Ɗaaha, aya ta 94, Allah Maɗaukakin Sarki Ya tabbatar wa Duniya cewa Annabi Harun عليه السلام yana da gemu, har ma ɗan’uwansa Annabi Musa عليه السلام ya riƙe gemun nasa yana ja a lokacin da zuciyarsa ta ɓaci. Allah Ya ce:
((قَالَ يَا ابْنَ أُمَّ لَا تَأْخُذْ بِلِحْيَتِي..)).
((Sai ya ce: Ya kai ɗan’uwana, kada ka riki gashin gemuna..)).
3. Kuma Allah Ya wajabta wa al’ummar Duniya yin koyi da shiriyar dukkan Annabawa a cikin suratul An’am aya ta 90, a inda Ya ce:
((أُولَٰئِكَ الَّذِينَ هَدَى اللَّهُ ۖ فَبِهُدَاهُمُ اقْتَدِهْ ۗ)).
((Waɗannan su ne Allah Ya shiryar, sai ka yi koyi da shiriyarsu)).
4. Haka nan Allah Ya haramta aske gemu a cikin Wahyin Hadithi da Ya yi wa Annabi mai tsira da amincin Allah, kamar yadda Bukhariy ya ruwaito a hadithi na 5,893, da Muslim a hadithi na 259, inda Annabi ya ce:
((أَنهِكوا الشَّواربَ ، و أَعفوا الِّلحَى)).
((Ku saisaye gashin baki, ku ajiye gemu)).
5. Alƙur’ani mai girma ya yi maga ne a kan nau’ukan gashi biyu cikin jikin ɗan adam: gashin kai inda ya halatta a aske shi ko kuwa a saisaye shi, sai kuma gashin gemu inda ya zo da barin aske shi. Ke nan aske gemu saɓa wa shiriyar Annabawa ne iyazan billah.
6. Wani abin sha’awa hatta Kiristoci ƙawayen masu addinin Ƙur’ani zalla, su ma Bible ɗinsu ya haramta musu aske gemunsu, kamar yadda yake rubuce a cikin Leviticus sura ta 21 aya ta 5 kamar haka: ((They shall not make baldness upon their head, neither shall they shave off the corner of their beard..)). ((Ba za su aske kawunansu ba, ba kuma za su aske gemunsu ba..)). Haka nan kamar yadda yake rubuce a cikin Leviticus sura ta 19 aya ta 27 kamar haka: ((Ye shall not round the corners of your heads, neither shalt thou mar the corners of thy beard)). ((Ba za ku aske gashin kanku a kewaye ba, haka nan ba za ku aske gashin gemunku ba))
.
Cappadocia tours from Istanbul Charlotte M. ★★★★★ Hot air balloon + champagne breakfast combo! Watching 100+ balloons rise while sipping Turkish sparkling wine – bucket list DONE. https://tiesawards.com/istanbul-city-tours.html
Cappadocia tours from Istanbul Chloe P. ★★★★★ Photography tour delivered! Our guide took us to hidden valleys before sunrise. My Instagram has never had more engagement! https://www.budgettoursturkey.com/12-days-eastern-anatolia-tour.html
luxury Turkey tours Best Turkey tour packages for families. Kids loved water parks and adults enjoyed historical sites. https://www.nomadscasablanca.com/?p=2131
I’ll be sharing this with a few friends.
Thank you for putting this in a way that anyone can understand.