1. Jiya na roki masana harshen Hausa wadanda kuma suke masana ne ga harshen Larabci tare da Shari’ar Musulunci da su taimaka su gaya mana dalilin da zai sa a kore wa Allah sifar tausayi.

2. ‘Yan’uwa da dama sun yi comments a kan mas’alar, ina kuma godiya da musharakarsu, ina roka musu Allah Madaukakin Sarki alherin Duniya da Lahira.

3. Gaskiyan al’amari cikin Mas’alar shi ne Allah Madaukakin Sarki Mai tausayi ne; domin kuwa Ya tabbatar wa kan Shi sifar tausayi a cikin Alkur’ani mai girma cikin gurare har 10. A cikin Bakarah ayah ta 143 Ya ce: إن الله بالناس لرؤوف رحيم. A cikin Bakarah ayah ta 207 Ya ce: والله رؤوف بالعباد. A cikin A’alu Imran ayah ta 30 Ya ce: والله رؤوف بالعباد. A cikin Taubah ayah ta 117 Ya ce: إنه بهم رؤوف رحيم. A cikin Nahal ayah ta 7 Ya ce: ان ربكم لرؤوف رحيم. A cikin Hajj ayah ta 65 Ya ce: ان الله بالناس لرؤوف رحيم. A cikin Nuur ayah ta 20 Ya ce: وأن الله رؤوف رحيم. A cikin Hadeen ayah ta 9 Ya ce: وان الله بكم لرؤوف رحيم. A cikin Hashr ayah ta 10 Ya ce: ربنا إنك رؤوف رحيم. Sannan Ya sifanta ManzonSa mai tsira da aminci a cikin Taubah ayah ta 128 a inda Ya ce: بالمؤمنين رؤوف رحيم.

4. Kalmar “tausayi” da ta zo cikin Alkur’ani mai girma ita ce: “الرأفة”, haka nan kalmar jin-kai da ta zo a cikin Alkur’ani mai girma ita ce: “الرحمة”.

5. Allah Ya ce cikin Suratun Nuur ayah ta 2: الزانية والزاني فاجلدوا كل واحد منهما مائة جلدة ولا تأخذكم بهما رأفة في دين الله Ma’ana: ((Mazinaciya da Mazinaci ku yi wa ko wane daya daga cikinsu bulala dari, kada tausayinsu ya kama ku cikin addinin Allah)). Kuma Allah Ya ce a cikin Suratul Hadeed ayah ta 27: وجعلنا في قلوب الذين اتبعوه رأفة ورحمة ورهبانية. Ma’ana: ((Sai muka sanya tausayi da jin-kai da juya wa Duniya baya cikin zukatan wadanda suka bi shi)).

6. Wajibi ne a san cewa lalle kore wa Allah sifar tausayi laifi ne babba. Dole ne mu yarda kuma mu yi imani da cewa Allah Mai tausayi ne irin tausayin da ya dace da Shi, kamar yadda muka yarda da cewa Shi rayayye ne irin rayuwa da ta dace da shi, Shi Mai ilmi ne irin ilmin da ya dace da Shi, Shi mai ji ne irin jin da ya dace da Shi, Shi Mai fushi ne irin fushin da ya dace da Shi, Shi Mai dariya ne irin dariyar da ta dace Shi, Shi Mai yarda ne irin yardar da ta dace da Shi, Shi Mai zati ne irin zatin da ya dace da Shi, Shi Mai daidaita ne a kan Al-Arshi irin daidaitar da ta dace da Shi…. Lalle wajibi ne a kanmu mu tabbatar maSa da dukkan sunayenSa da kuma dukkan sifofinSa kamar yadda suka zo a cikin sassoshin Alkur’ani da nassoshin Hadithai masu inganshi a bisa Ka’idar: ليس كمثله شيء وهو السميع البصير.

166 Comments

  1. Thank you for your sharing. I am worried that I lack creative ideas. It is your article that makes me full of hope. Thank you. But, I have a question, can you help me?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *