TABBAS DA ‘YAN BIDI’A JARUMAI NE SU A CIKIN ILHADINSU, TOH DA DA ALLAH NE YA KAMATA SU FARA:

  1. Dukkan wasu jahilai, ko wasu ‘yan bidi’ah, ko wasu ‘yan bin adifah, ko wasu masu ilhadi da suke zagin wani mutum a wannan zamani namu a kan cewa ya ce: Mahaifin Annabinmu, Annabi Muhammad mai tsira da aminci yana cikin Wuta, ko a kan cewa ya ce: Allah Madaukakin Sarki Ya hana shi Annabinmu, Annabi Muhammad mai tsira da aminci nema wa mahaifiyarsa gafarar Allah, toh da dukkan wadannan nau’ukan mutane da na ambata suna da adalci, ko da suna da jarunta toh da kuwa tabbas da Allah Madaukakin Sarki ne za su fara wannan zagi nasu, sannan su biyunta da ManzonSa, Annabinmu, Annabi Muhammad mai tsira da aminci, sannan su ukunta da Sahabbai, sannan su hudunta da Tabi’ai, sannan su biyartar da Tabi’ut Tabi’in, sannan su gangaro zuwa ga su Imam Muslim da tsaransa, da kuma wadanda suke a tsarin almajiransa, sannan su kara gangarowa har zuwa wadanda suke cikin wannan zamani namu.
  2. Dalilin da zai sa su yi haka kuwa shi ne: Allah Madaukakin Sarki ne ya yi wa Annnabi Muhammad wahayin cewa mahaifin shi Annabi Muhammad din yana cikin Wuta, Shi ne kuma Madaukakin Sarki Ya hana shi Annabi Muhammad nema wa mahaifiyarsa gafararSa, daga nan kuma shi Annabi ya isar da wannan wahayin zuwa ga sahabbansa su kuwa sahabbai suka isar da shi zuwa ga Tabi’ai su kuwa Tabi’ai suka isar da shi zuwa Tabi’ut Tabi’in, har dai aka isar da shi wannan wahayin zuwa ga su Imamu Muslim da na bayansu, har kuma zuwa garemu mu ma a wannan zamanin.
  3. Ke nan da dai ‘yan bidi’ah wasu mutane ne da suke da adalci da jarunta toh da kuwa Allah Madaukakin Sarki ne za su fara zaga karara, sannan su zagi Annabi, sannan su zagi Sahabbai da Tabi’ai, sannan su zagi na kasa da wadannan kafin su kai ga zagin mutanen wannan zamani namu, toh amma da yake su lalatattu ne ragwaye shi ne ya sa suke bugun guzuma su bar karsana.
  4. Allah Ubangijinmu muke rokon Ya tabbatar da dugaduginmu a kan mika wuya gare Shi, da yin biyayya gare Shi tare da ManzonSa Annabi Muhammad mai tsira da aminci tare da iyalansa da sahabbansa, da yin imani da dukkan abin da ManzonSa ya zo mana da shi sawaa’un ya dace da son zuciyarmu ko kuwa ya saba da son zuciyarmu. Ameen.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *