Tambaya ga ‘yan ƙalaƙato masu ƙaryata wahayin Hadithi cewa shin idan suka fara salla daga lokacin da Rana ta karkata daga tsakiyar sama ba sa dainawa ne sai in dare ya yi duhu tukun??
Domin Alkur’ani dai ya ce  cikin Suratul Isra’i aya ta 78:
أقم الصلاة لدلوك الشمس إلى غسق الليل

Ma’ana: “Ka tsayar da salla daga karkatar Rana har zuwa duhun dare”.
In kuma suna dainawa to da wace ayah ce suka dogara da ita wacce ta shafe zahirin wannan ayah ta Suratul Isra’i? Lalle muna neman amsa daga ‘yan kalakaton Duniya gaba daya.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *