1. A ranar 04/12/1977 M ne, wanda ya dace da 23/12/1397 H, Group ɗin masu da’awah zuwa ga yin riƙo da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah a garin Jos da kewaye suka yi taro cikin garin Jos a office ɗin sakataren group ɗin Sheikh Yahya Aga Abubakar, a kuma ƙarkashin jagoran Group ɗin Sheikh Garba Fasali, sun ƙira taron ne domin zaɓen sunan da zai dace da ƙungiyar da’awah mai rajista da suke da niyyar kafawa.
2. Mutane da yawa sun ɗaga hannu sun ba wa jagorancin Group ɗin sunan da suke ganin ya dace a sanya wa sabuwar ƙungiyar da ake son kafawa; wasu suka ce sunan ya kasance: Ath-Thaƙafatul Islamiyyah الثقافة الاسلامية. Wasu suka ce: Zaharal Haƙ ظهر الحق. Wasu suke ce: Al-Aƙidatus Sahihah العقيدة الصحيحة. Wasu suka ce: Nurul Islam نور الاسلام. Toh amma sai Sheikh Isma’ila Idris ya ɗaga hannu ya ce shi yana ganin zai fi dacewa a sanya wa ƙungiyar suna: Izalatul Bid’ah ازالة البدعة. Sai taro ya rinjayar da wannan shawara ta Sheikh Isma’ila Idris.
3. Toh amma bayan shugabannin wannan Group na da’awah sun je gaban Sheikh Abubakar Mahmud Gumi a garin Kaduna sun shaida masa abin da ya faru sai ya ba su shawarar cewa sunan ƙungiyar ya kamata ya zamanto: Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iƙamatis Sunnah جماعة ازالة البدعة واقامة السنة aka kuma yi aiki da wannan shawara ta Sheikh Abubakar Mahmud Gumi aka bayyanar da wannan sunan a ranar kafa Ƙungiyar