YANA DAGA CIKIN MASU BAIWAR FIRASAH:

Shaikhul Islam Ibnu Taimiyyah yana daga cikin Salafus Salih da mabiyansu masu baiwar Firasah, ko Tawassum. Sahabbai da Tabi’ai da Tabi’ut Tabi’in, da na bayansu da yawa ne aka samu wadanda suke da Firasah ko Tawassum; ma’anar haka kuwa shi ne: wani mutumin kirki mai riko da Sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ya fadi wani abu, kuma a cikin baiwar Allah sai ka ga  kuma abun ya kasance kamar yadda ya fada din, ba ragi ba kari. Daga cikin Sahabbai ga wasu masu Firasah da Tawassum a nan:-

1. Sahabi Umar Bin Khattab ya taba ganin Ashtar, sai ya ce wannan zai zamo wa Musulmi fitina a nan gaba. Haka kuma ya kasance.
2. Wata rana Sahabi Anas ya je kasuwa ya kuma kalli wata mata, da ya zo gun Sahabi Uthman Bin Affan sai shi Uthman ya ce da shi: Dayanku ya kan shigo inda nake alhali akwai alamar zina a idonsa! Sai Anas ya ce: Wahayi ne aka samu bayan Manzon Allah? Sai ya ce: A’a hujjace da firasah.
3. Sahabi Ibnu Abbas yana cewa: Ba wanda zai tambaye ni wani abu face na fahimci cewa faqihi ne shi ko kuwa ba faqihi ba ne.
4. Sahabi Jundub Bin Abdillah ya ji wani yana karatun Alkur’ani, sai ya ce: Sam wannan ba mutumin kirki ba ne. Haka kuwa aka yi ba a jima ba sai aka gan shi yana jagorantar Khawarijawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *