1. Duk wani jahilin barafidhen da ya ce wa Duniya cewa: Hafsu, ko A’asim ‘yan shi’ah ne rafidha, to Ahlus Sunnah suna neman sa da abu biyu:
Na farko: ya kawo wa Duniya inda littatafan Jarhu wat Tadil, da kuma littattafan Tarajumur Rijal na Ahlus Sunnah suka ce Hafsu, ko Malaminsa A’asim ‘yan shi’ah ne rafidha. Wannan na farko ke nan.
Na biyu: Idan wadannan jahilan ‘yan shi’an suka kasa kawo abin da muka neme su da su kawo shi daga littattafanmu na Ahlus Sunnah Wal Jama’ah, toh sai mu ce musu su ma kawo mana daga cikin yardaddun littattafansu na Kutubur Rijal; kamar su: Rijaalul Kishshiy رجال الكشي da Rijalut Tuusiy رجال الطوسي ko waninsu, mu gani ko su wadannan littattafan suna lissafta  Hafsu da A’asim cikin mazajen shi’ah rafidha?? Tabbas sam ba za su iya kawowa ba sai dai kawai su yi hayaniya da fagauniya.

2. Sannan wani abu da ya kamata wadannan jahilan rafidhawa su kara sani shi ne:  Kashshiy الكشي da Najashiy النجاشي da Ibnu Dawud Al- Hilliy ابن داود الحلي da Khaaqaaniy الخاقاني da Buriy البرقي sam ba su ambaci Hafsu cikin mazajensu a cikin littattafansu na Tarajumur Rilaj a gurin shi’ah rafidha.

3. Abin da kawai ya faru shi ne: Tuusiy ya ambaci shi Hafsu a lamba ta 181 cewa shi ma ya yi karatu a gurin Ja’afarus Sadiq جعفر الصادق masu nakaltowa daga Tuusiy watau Qahbaa’iy القهبائي da kuma Haa’iriy الحائري su ma sun ambaci hakan. Kuma shi da ma Tuusiy ba dukkan wanda ya ambata cikin littafinsa ba ne yake dan shi’ah rafidha, a’a, kamar yadda Tusturiy ءاية الله التستري ya ce shi Tuusiy har ma nawasib ya ambata a cikin littafin Rijal dinsa.

4. Sannan har yanzu Ayatullah Tustury ءاية الله التستري ya sake cewa a littafinsa Qamusur Rijal 1/29, da 1/180 ambaton wani mutum da Tuusiy zai yi a cikin littafin Rijal dinsa ba ya nuna cewa shi amintacce ne, haka nan ba ya nuna cewa shi yana daga cikin Shi’ah.

5. Haka nan har yanzu Shi Tuusiy ya lissafta Ahmad Bin Khaseeb أحمد بن الخصيب cikin daliban Al-Haadiy الهادي duk kuwa da cewa shi احمد بن الخصيب nasibi ne.

6. Abu na karshe da zan ce a nan shi ne: Abu ne mai kyau Duniya ta san cewa: ba dukkan wanda ya yi karatu ko ya yi ruwayah a gurin Sahabi Aliyyu Bin Abi Talib ba, ko a gurin Tabi’i kamar Ja’afarus Sadiq ba ne yake zama dan bidi’ar shi’ah rafidha. Misali shi جعفر الصادق Tabi’i ne salihi kuma babban malami mai almajirai da yawa, ya rasu a shekarar hijira 148, su Abu Hanifah da Malik dukkansu sun yi karatu  da ruwayah a gurinsa kamar yadda suka yi karatu da ruwayah a gurin wasunsa. Saboda haka kasancewar wani ya yi ruwayah ko ya yi karatu a gurin Ja’afarus Sadiq sam ba ya nuna cewa shi dan shi’ah ne barafidhe. Babu mai fadin haka sai wanda jakin gidansa ya fi shi hankali.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *