Kungiyanci shi ne Ta’assubanci, shi kuwa Ta’assubanci yana nufin mutum ya watsar da gaskiya ya dauki karya saboda kawai son zuciya.

Kuma shi Ta’assubanci (kungiyanci) kusan yana iya shiga cikin dukkan wani al’amari da ya shafi dangantakar mutane da ‘yan’uwansu mutane. Misali: kana iya yin kungiyanci watau ta’assubanci a kana majalisinka, ko a kan kungiyarka, ko a kan malaminka, ko a kan makarantarka, ko a kan garinka, ko a kan shugabanka, ko a kan kabilarka, ko a kan ‘ya’yanka, ko a kan iyayenka, ko a kan danginka, ko a kan wasu abubuwa masu kama da haka.

Yana da kyau a san cewa ita Shari’ar Musulunci ba za ta haramta maka yin malami ba saboda kawai kasancewar yin ta’assubanci a kan malami haramun ne. Haka nan ba za ta haramta maka danganta kai zuwa ga wani majilisi ba, ko kafa wani majilisi ba saboda kawai yin ta’assubanci a kan majilisi haramun ne. Hakan nan ba za ta haramta maka danganta kai zuwa ga kungiya ba, ko kafa kungiya ba saboda kawai yin ta’assubanci a kan kungiya haramun ne.

Abin da Shari’ar Musulunci za ta yi maka shi ne ta ce maka: Yin malami halal ne, amma kuma yin ta’assubanci ko kungiyanci a kan malami haramun ne. Ta kuma ce maka yin majilisi halal ne, amma kuma yin ta’assubanci ko kungiyanci a kan mijilisi haramun ne. Ta kuma ce maka yin kungiya ko jama’a halal ne, amma kuma yin ta’assubanci ko kungiyanci a kan kungiya, ko a kan jama’a haramun ne.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *