1. Kungiyanci yana nufin take Shari’ah, ko saba wa Shari’ah domin tabbatar da wata manufa ta kungiyarka.

2. Amma kafa kungiya, ko kasancewa memba cikin wata kungiya domin tabbatar da wata halastacciyar maslaha wannan halal ne, babu mai musun halaccin hakan sai wanda ya kasa jakin gidansa tunani.

3. Kana iya kirga gwamman kungiyoyi a kasashen Duniya daban daban wadanda bangarorin mutane daban daban suka kafa domin kokarin tabbatar da wata ayyanannar maslaha karbabba a idanun Shari’ah, wasu kungiyoyin na Mujtahidai ne zalla, wasu kuwa na sarakunan Musulmi ne zalla, wasu kuwa na ‘yankasuwan Musulmi ne, wasu kuwa na kowa da kowa ne cikin al’ummar Musulmi; ke nana babu mai fitowa ya gaya wa Duniya cewa kafa kungiya ko ma wace iri ce abu ne da yake haram sai jahili murakkabi ko kuwa mai bin son zuciyarsa.

204 Comments

  1. I don’t think the title of your article matches the content lol. Just kidding, mainly because I had some doubts after reading the article.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *