Wani Dan bidi’ar kalakato ya tambaye ni a page dina na Facebook cikin daren da ya gabata kamar haka:
Na daya: Kawo mini sunan Mala’ikan da Allah Ya aiko shi ya kawo wa Annabi Hadithi?
Na biyu: Kawo mini Hadithin da ya zo da umurnin raka’o’in salla.
Amsa a kan tambayar farko ita ce: Shi dai Wahayi ya kan zo wa Annabi mai tsira da amincin Allah ne ta hanyoyi daban daban, cikinsu kuwa har da magana da Shi Allah Zai yi da Annabi kai tsaye ta bayan hijabi. Amma a mafi yawan lokuta Mala’ika Jibril ne Allah ya fi turawa zuwa ga shi Annabin. Kuma yadda Mala’ika Jibril yake yi wa Annabi wahyin Alkur’ani haka ma yake yin masa wahyin Hadithin. Akwai hujjoji Masu yawa a kan wannan amma ga kadan daga cikinsu: Imamush Sha’fi’iy ya ruwaito cikin Musnad dinsa Hadithi na 1,798, da Bazzar cikin Musnad dinsa Hadithi na 2,914, da Ibnu Abi Shaibah cikin Musannaf dinsa Hadithi na 34,332, da Ibnu Nu’aim cikin Hilyah Hadithi 10/26, da Baihaqiy cikin Shu’abul Iman Hadithi na 1,141, da kuma cikin Al-Asma’u Was Sifat Hadithi na 427, da Shihabul Qudha’iy cikin Musnad dinsa Hadithi na 1,151, da Ibnu Abi Bashran cikin Amaliy Hadithi na 1,411, da Bagwiy cikin Sharhus Sunnah Hadithi na 4,111, da Ibnu A’amir cikin Jami’insa Hadithi na 20,100, duk wadannan sun ruwaito Hadithin daga Sahabi Ibnu Mas’ud, da Huzaifah Ibnul Yaman, da Jabir, da Abu Umamah cewa: Annabi mai tsira da amincin Allah ya ce:-
((إنه ليس شيء يقربكم الى الجنة الا قد امرتكم به وليس شيء يقربكم الى النار الا قد نهيتكم عنه إن روح القدس نفث في روعي إن نفسا لا تموت حتى تستكمل رزقها فاتقوا الله وأجملوا الطلب)).
Ma’ana: ((Babu wani abu da zai kusantar da ku zuwa ga Aljanna face na umurce ku da shi, babu wani abu da zai kusantar da ku zuwa Wuta face na hana ku shi. Lalle Ruhul Qudus (Mala’ika Jibril) ya busa a cikin zuciyata cewa wata rai ba za ta mutu ba har sai ta cika arzikinta, ku ji tsoron Allah ku kyautata nema)). Albaniy ya inganta wannan Hadithi a cikin Silsila Sahiha 6/865, number 2,866, da kuma Sahihul Jami’is Sageer 1/419, number 2,085. Kun ga anan Annabi ya fito karara ya ce wa Duniya Mala’ika Jibril ne ya kawo masa wannan magana a cikin zuciyarsa.
Hadithi na biyu shi ne: Hadithin da Muslim ya ruwaito number na 8, da Abu Dawud na 4,695, da Tirmiziy na 2,610, da Ibnu Majah na 63, da Ahmad na 367 daga Sahabi Umar Bin Khattab Allah Ya kara masa yarda ya ce:-
((بينما نحن جلوس عند رسول الله صلى الله عليه واله وسلم ذات يوم اذ طلع علينا رجل شديد بياض الثياب شديد سواد الشعر لا يرى عليه أثر السفر ولا يعرفه منا أحد حتى جلس إلى النبي فأسند ركبتيه إلى ركبتيه ووضع كفيه على فخذيه وقال: يا محمد أخبرني عن الاسلام فقال رسول الله الاسلام ان تشهد ان لا اله الا الله وان محمدا رسول الله وتقيم الصلاة وتوتي الزكاة وتصوم رمضان وتحج البيت ان استطعت اليه سبيلا. قال صدقت قال فعجبنا له يسأله ويصدقه قال فأخبرني عن الإيمان قال ان تؤمن بالله وملائكته وكتبه ورسله واليوم الآخر وتؤمن بالقدر خيره وشره قال صدقت. قال فأخبرني عن الإحسان قال ان تعبد الله كانك تراه فان لم تكن تراه فانه يراك. قال فأخبرني عن الساعة قال ما المسؤول عنها باعلم من السائل قال فأخبرني عن أمارتها قال ان تلد الأمة ربتها وان ترى الحفاة العراة العالة رعاء الشاء يتطاولون في البنيان قال: ثم انطلق فلبثت مليا ثم قال لي: يا عمر اتدري من السائل؟ قلت الله ورسوله أعلم قال فانه جبريل اتاكم يعلمكم دينكم)).
A cikin wannan Hadithi Annabi mai tsira da amincin Allah ya bayyanar da cewa Jibril ya zo masa cikin siffar mutum, ya kawo masa wannan wahyin domin koya wa Musulmi addininsu. Watau ya tambaye shi sannan kuma ya cusa masa amsar tambayar shi kuma ya ba da amsar bayan Jibril ya yi masa wahyinta.
AMSAR TAMBAYA TA BIYU:
Amsa a kan tambayarsa ta biyu: Watau: Kawo mini hadithin da ya zo da umurnin raka’o’in salla.
Farko dai sai a cewa wannan dan kalakato ya yi gwaranci da ya ce: “da ya zo da umurnin”. Lalle in da shi wannan dan kalakaton malami ne da sai ya ce: “Hadithin da ya zo da raka’o’in salla”; domin wannan jumla ta fi zama jami’ah; saboda ayah ta 7 cikin Suratul Hashri inda Allah ya ce wa al’ummar Duniya:-
((وما ءاتاكم الرسول فخذوه وما نهاكم عنه فانتهوا)).
Ma’ana: ((Duk abin da Manzon ya ba ku, toh ku karbe shi, duk kuma abin da ya hana ku yin sa toh ku hanu)). Sai Allah ya yi amfani da lafazin: “Duk abin da ya baku” ma’ana Duk abin da ya zo muku da shi sai ku rike shi domin ya zama Shari’ar Musulunci, da ma kuma Allah ya ce: Hakika Manzon Allah ya kasance muku abin koyi mai kyau.
Na biyu kuma: Sa a ce da shi wannan dan kalakaton: Lalle Hadithai da dama ne suka zo da yin sallolin farilla raka’o’i 17 a cikin dare da rana watau a cikin awa 24, ga ma biyu kacal daga cikinsu da zan ambata wa Duniya:-
1. Buhariy ya ruwaito hadithi na 350, da Muslim na 685 daga Nana A’isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((فرض الله الصلاة حين فرضها ركعتين ركعتين في الحضر والسفر فاقرت صلاة السفر وزيد في صلاة الحضر)).
Ma’ana: ((An farlanta Salla ne a lokacin da aka farlanta ta a matsayin raka biyu biyu a yanayin zaman gida da kuma yanayi na tafiya (in banda sallar magariba, ita wannan dama raka’anta uku ne ba a kuma canja ba har abada) toh sai aka tabbatar da sallar tafiya a kan raka’a biyu boyun, aka kuma kara raka’o’i a yanayin zaman gida)).
2. Tahaawiy ya ruwaito cikin Sharhu Ma’anil A’athar Hadithi na 4,260, da Baihaqiy cikin Sunanul Kunraa Hadithi na 1,698 da isnadi sahihi daga Nana A’isha Allah Ya kara mata yarda ta ce:-
((ان أول ما فرضت الصلاة ركعتين ركعتين فلما قدم النبي صلى الله عليه وسلم المدينة واطمأن زاد ركعتين غير المغرب لأنها وتر وصلاة الغداة لطول قراءتها. قالت وكان اذا سافر صلى صلاته الاولى)).
Ma’ana: ((Lalle farkon farlanta salla da aka yi raka’o’i biyu biyu ne, toh a lokacin da Annabi ya dawo Madina ya kuma nitsu, sai ya kara biyu banda a sallar magariba; domin ita magariba da ma ita mara ce, banda kuma sallar Asuba saboda tsawon karatunta. Sai ta ce: Ya kasance idan ya yi tafiya sai ya rika yin sallarsa ta farko)). Watau Asuba raka’a 2, Azahar raka’a 2, La’asar raka’a 2, Magariba raka’a 3, Isha’i raka’a 2. Ke nan raka’o’in sallolin farilla a halin tafiya 11 ne. Amma a halin zaman gida raka’o’in 17 ne: Asuba 2, Azahar 4, La’asar 4, Magriba 3, Isha 4. Abin da wadannan Hadithai biyu da na ambata yanzu suke koya wa al’ummar musulmin Duniya. Akwai kuma wasu hadithan da yawa banda wadannan su ma bayanin da suke yi ke nan.
Abu na karshe shi wannan dan kalakaton ya ce suna da wasu Hadithai har 10, wadanda in sun kawo su toh al’ummar Musulmi ba za su iya kare gaskiyarsu ba!! Haka shi wannan dan bidi’ar ya ce. Don Allah in rokon ‘Yan’uwa a duk inda suke da su matsa wa ‘yan bidi’ar kalakato domin su kawo wa Duniya nassin wadannan Hadithai 10 din, in kuma sun kawo su, toh mu kuwa in sha Allah za mu ba su amsa a kansu; domin Duniya ta gani.
**sleep lean**
sleeplean is a US-trusted, naturally focused nighttime support formula that helps your body burn fat while you rest.