DORA DAMA A KAN HAGU CIKIN SALLA SHI NE SUNNAH, SAKIN HANNAYE CIKIN SALLA SABANIN SUNNAH NE

Imamush Shaukaanii ya ce cikin littafinsa Nailul Autaar 2/205: ((Hadithan dora dama a kan hagu ishrin ne suka zo daga Annabi mai tsira da amincin Allah ta hanyar
mutum goma sha takwas, tsakanin Sahabi da Tabi’i)).

Ga wasu daga cikin hadithan da Imamush Shaukaanii ya yi
maganarsu:-

1- Imamu Muslim ya ruwaito hadthi na 401 cewa: Annabi mai tsira da amincin Allah:

((Ya kasance yana
dora hannun damansa a kan
hagunsa)).

2- Imamul Bukharii ya ruwaito hadithi na 740 da Imam Malik cikin Muwattaa hadithi na 546 cewa
Manzon Allah mai tsira da amincin Allah yana umurtan sahabbansa da dora dama a kan hagu:

((Mutane sun kasance ana
umurtan su da cewa: mutum ya dora damansa a kan zira’insa na hagu a cikin Salla)).

3- Imamut Tabaraanii ya ruwaito cikin Almu’ujamul Kabiir hadithi na 11,323, da Imamud Daara Qudnii cikin Babun Fi Akhzish Shimaal Bil
Yamiin hadithi na 3, da Imam Ibnu Hibbaan dadithi na 1,770, da Imam Sulaimaan Ibnu Dawud Attayaalisii
cikin Musnad hadithi na 2,776 cewa Annabi mai tsira da amincin Allah ya kasance yana cewa:

((Mu taron Annabawa an umurce mu da gauggauta buda-baki, da jinkirta sahur, da kuma mu dora hannayenmu na dama a kan
hannayenmu na hagu)).

Albaanii ya inganta hadithin cikin Sahihul Jami’is Sagiir 1/454.

4- Imam Ahmad ya ruwaito hadithi na 15,090, da Imam Abu Dawud Hadiyhi na 755, da isnadi sahihi cewa Manzon Allah mai tsira da
amincin Allah ((Ya wuce wani
mutum yana salla amma ya dora hannunsa na hagu a kan na dama, sai ya balle hannun ya dora daman
a kan hagun)).

5- Imam Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 727, da Imam Nasa’ii hadithi na 963, da Imam Ibnu Khuzaimah hadithi na 480 da isnadi sahihi cewa Manzon Allah
mai tsira da amincin Allah

((Ya kasance yana dora dama a kanbayan tafinsa na hagu, da kuma wuyan hannu, da dantse)).

6- Imama Abu Dawud ya ruwaito hadithi na 759, da Imam Ibnu Khuzaimah hadithi na 479 cewa
Annabi mai tsira da amincin Allah

((Ya kasance yana sanya hannun damansa a kan hagunsa, sannan sai ya hada tsakaninsu a kan kirjinsa alhalin yana cikin salla)).

TAMBAYOYI TARE DA
AMSOSHINSU:

(1) Idan wani ya ce: Amma kuma ai Imamut Tabarii ya ruwaito cikin littafinsa Almuujamul Kabiir hadithi
na 16,563, daga Sahabi Mu’azu Dan Jabal ya ce:-

(( ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺻﻼﺗﻪ ﺭﻓﻊ ﻳﺪﻳﻪ ﻗﺒﺎﻟﺔ ﺃﺫﻧﻴﻪ، ﻓﺈﺫﺍ ﻛﺒﺮ ﺍﺭﺳﻠﻬﻤﺎ، ﺛﻢﺳﻜﺖ، ﻭﺭﺑﻤﺎ ﻳﻀﻊ ﻳﻤﻴﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﻳﺴﺎﺭﻩ )).

Ma’ana: ((Annabi mai tsira da
amincin Allah ya kasance idan yana cikin sallarsa sai ya daga hannu daura da kunnensa, idan ya yi kabbara sai ya sake su, sai kuma ya yi shiru, wani lokaci ma
nakan gan shi yana dora damansa a kan hagunsa)).

Wannan hadithi
ai shi ne hujjar sake hannu!!
Sai a ce da shi: Da farko dai ya kamata ka san cewa wannan hadithi maudhuu’i ne, watau hadithi ne da cikin isnadinsa akwai makaryaci kazzaabi wannan kuwa
shi ne: Khasiib Bin Jahdar, ya zo cikin littafin Miizaanu Litidaal 1/653
kamar haka:-

(( ﺍﻟﺨﺼﻴﺐ ﺑﻦ ﺟﺤﺪﺭ: ﻋﻦ ﻋﻤﺮﻭ ﺑﻦ ﺩﻳﻨﺎﺭ، ﻭﺃﺑﻲ ﺻﺎﻟﺢ ﺍﻟﺴﻤﺎﻥ، ﻛﺬﺑﻪ ﺷﻌﺒﺔ ﻭﺍﻟﻘﻄﺎﻥ ﻭﺍﺑﻦ ﻣﻌﻴﻦ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﺣﻤﺪ: ﻻ ﻳﻜﺘﺐ ﺣﺪﻳﺜﻪ. ﻭﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺨﺎﺭﻱ: ﻛﺬﺍﺏ
ﺍﺳﺘﻌﺪﻯ ﻋﻠﻴﻪ ﺷﻌﺒﺔ)).

Ma’ana: ((Khasiib Bin Jahdar: daga Amr Bin Diinaar, da Abu Salihis Sammaan: Shu’ubah, da Qattaan, da Ibnu Ma’iin sun karyata shi.
Ahmad ya ce: Ba a rubuta
hadithinsa. Bukharii ya ce:
Makaryaci ne, Shu’ubah ya yi
bayanin karyarsa))

Na biyu: Da za a kaddara cewa hadithin ingantacce ne, to da sai a fassara shi da cewa: yana nufin
bayan Annabi ya daga
hannayensa daura da kunnuwansa lokacin kabbarar harama, ya kan
sake hannayen nasa ne zuwa
kirjinsa, dole a yi irin wannan
fassarar saboda hadithin ya dace da sauran hadithai ingantattu cikin babin.

Babban masanin ilmin hadithi Alhaafiz Ibnu Hajar ya ce cikin littafinsa: Attalkhiisul Habiir 1/554:-

(( ﺗﻨﺒﻴﻪ: ﻗﺎﻝ ﺍﻟﻐﺰﺍﻟﻲ: ﺳﻤﻌﺖ ﺑﻌﺾ ﺍﻟﻤﺤﺪﺛﻴﻦ ﻳﻘﻮﻝ: ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺨﺒﺮ ﺍﻧﻤﺎ ﻭﺭﺩ ﺑﺎﻧﻪ ﻳﺮﺳﻞ ﻳﺪﻳﻪ ﺍﻟﻰﺻﺪﺭﻩ، ﻻ ﺍﻧﻪ ﻳﺮﺳﻠﻬﻤﺎ ﺛﻢ ﻳﺴﺘﺄﻧﻒ ﺭﻓﻌﻬﻤﺎ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ. ﺣﻜﺎﻩ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﺼﻼﺡ ﻓﻲ ﻣﺸﻜﻞ ﺍﻟﻮﺳﻴﻂ )).

Ma’ana: ((Fadakarwa: Gazaalii ya ce: Na ji sashin malaman hadithi na cewa: Wannan hadithi ya zo ne
a kan cewa yana sake hannayensa ne zuwa girjinsa, ba wai yana sake su ba ne, sannan daga baya ya daga su zuwa girji ba. Ibnus Salaah ya hikaito shi cikin
“Mushkilul Wasiit”)).

(2) Idan wani kuma ya ce: To ai an samu daga cikin magabata wadanda suka yi salla hannayensu
a sake, don mene ne za a ce da mu yanzu: ba za mu yi salla hannayenmu a sake ba?
To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san cewa ya kai dan’uwa! Annabi Muhammad mai tsira da amincin Allah shi ne kadai
wanda Allah Ya aiko shi zuwa gare ka, bai aiko waninsa zuwa gare ka ba a matsayin manzo, saboda haka ba daidai ba ne ka bar umurninsa shi Annabi Muhammad ko kuma ka bar aikinsa, sannan ka je kana riko da umurni ko da aikin
wani koma wane ne shi a wannan duniya!

Abu na biyu: A lokacin da Sahabi Abdullahi Dan Abbas ya yi yunkurin tabbatar da sunnar tamattu’i cikin Hajji, an samu wasu mutane da suka ce da shi: Ai Abubakar da Umar sun hana Mut’ar Hajji, shi kuwa sai ya amsa
ya ce da su:

((Wani dutse ya yi kusan sauko muku daga sama! Ina
ce muku: Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ya ce, sannan kuna ce da ni: Abubakar da Umar
sun ce!)).

Wannan magana ta Abdullahi Dan Abbas asalinta na cikin Musnadu Ahmad hadithi na 3,121, da Almuujamul Ausat na Tabaraanii hadithi na 21, da Jami’u bayanil ilmi na Ibnu Abdil Bar hadithi na
2,377, da Alfaqih wal Mutafaqqih na Khatiibul Bagdaadii hadithi na 380.

Abu na uku shi ne: Barin aiki da maganar Annabi ko aikinsa zuwa yin aiki da maganar wani ko aikinsa saba wa Ijma’in Al’ummah
ne, shi kuwa yin hakan haramun ne a bisa ittifakin dukkan malaman Duniya, idan Annabi ya yi umurni
da a yi Kablu a cikin salla sannan ka ji wani kuma yana cewa a yi sadlu domin ai sadlu ba ya bata salla to lalle wannan mutum ya yi haramun ya zama mai sabon Allah a bisa ijma’in Maluman Musulunci!

Ya zo cikin littafin Iiqazul Himam shafi na 68 cewa Imamush Shafi’ii ya ce:

((Musulmi sun yi Ijma’i a kan
cewa duk wanda sunnar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah ta bayyana gare shi, to, ba ya halatta
gare shi ya bar ta saboda yin riko da maganar wani)).

(3) Idan wani ya ce: To ai sake hannaye cikin salla shi ne mazhabar Imam Malik, tunda mu kuwa Malikiyyah ne ke nan dukkan
abin da Imam Malik ya yi na Addini shi ne mu ma za mu yi!!

To sai a ce da shi: Na farko dai ya kamata ka san cewa Allah Madaukakin Sarki bai aiko maka Imam Malik a matsayin manzo ba, a’a Ya aiko maka Annabi Muhammad ne a matsayin manzo zuwa gare ka kai da sauran mutanen Duniya baki daya, shi kuwa Annabi Muhammad babu inda ya ce da kai ka yi salla hannayenka a sake, a’a abin da ya ce da kai shi ne: Ka dora damanka
a kan hagunka cikin sallanka.

Takaka za ka bar nasa ka riki na wani komin girmansa kuwa a idanunka?

A bu na biyu: cewa da ka yi:
mazhabar Imam Malik ita ce: yin salla hannaye a sake, magana ce mara dikka, saboda shi Imam Malik
yana da fatawowi daidai har guda hudu ne cikin wannan mas’alar, ba wai fatawa daya kawai ba.

Babban Malami cikin mazhabar malikiyyah Imamul Baajii ya ce cikin littafinsa Almuntaqaa 1/281:

Imam Malik yana da fatawowi hudu da aka ruwaito daga gare shi cikin
wannan mas’alar:

Fatawar farko:
Ash’hab ya ruwaito daga gare shi cewa:

Babu laifi a dora dama a kan
hagu cikin sallar nafila da farilla.

Fatawa ta biyu: Mutarrif da Ibnul Maajishuun da kuma almajiransa na Iraq sun ruwaito daga gare shi
cewa: Dora dama a kan hagu cikin salla mustahabbi ne.

Fatawa ta uku:
Mutanen Iraq sun ruwaito
daga Malikawa daga shi Imam Malik cewa: Kada a dora dama a kan hagu cikin salla.

Fatawa ta
hudu: Ibnul Qaasim ya ruwaito daga gare shi cewa: makruuhi ne a
dora dama a kan hagu cikin sallar farilla, amma babu laifi a yi hakan cikin sallar nafila.
A nan ai kun ga ya kamata a ce imma Malikiyyar za a yi, to sai a yi wacce ta dace da sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah, ba wai
wacce ta saba wa sunnar
Muhammadur Rasuulul Lahi ba, Allah ya taimake kan yin aiki da sahihiyar Sunnar ManzonSa.

(4) Idan wani ya ce: To mene ne fahimtar Malamanmu na Da’awah da Aqidah kuma cikin wannan mas’alar?

Sai a ce da shi: Fahimtar mutanen da muka sani daga cikinsu ita ce:

Yin salla hannaye a sake abu ne da yake sabanin Sunnah. Misali:

Sheik Abdulaziz Bin Baz ya cecikin littafinsa na fatawa 11/144:-

(( ﺍﻟﺜﺎﺑﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺍﻧﻪ ﻳﻘﺒﺾ ﻳﺪﻳﻪ ﺣﺎﻝ ﻗﻴﺎﻣﻪ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ… ﺍﻣﺎ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻓﻤﻜﺮﻭﻩ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ ﻟﻜﻮﻧﻪ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ )).

Ma’ana: ((Abin da ya tabbata daga Annabi mai tsira da amincin Allah shi ne cewa: Yana kame hannayensa ne lokacin da yake tsaye cikin salla ..Amma sake
hannaye a cikin salla makruhi ne, yin sa bai kamata ba, saboda kasancewarsa sabanin Sunnah)).

Sannan ya sake cewa cikin
wannan littafin nasa 11/145:-

(( ﻭﺑﻤﺎ ﺫﻛﺮﻧﺎﻩ ﺗﻌﻠﻤﻮﻥ ﺍﻥ ﺇﺭﺳﺎﻝ ﺍﻟﻴﺪﻳﻦ ﻻ ﻳﻘﺪﺡ ﻓﻲ ﺍﺳﻼﻡ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ، ﻭﻻ ﻓﻲ ﺍﻛﻞ ﺫﺑﻴﺤﺘﻪ ﻟﻜﻨﻪ ﻣﻜﺮﻭﻩ ﻭﻣﺨﺎﻟﻒ ﻟﻠﺴﻨﺔ ﻻ ﻳﻨﺒﻐﻲ ﻓﻌﻠﻪ )).

Ma’ana: ((Saboda abin da muka ambata din nan ne za ku san cewa: Sake hannaye ba ya soke Musuluncin Musulmi, haka nan cin
yankansa, sai dai kuma shi
makruhi ne, kuma abu ne da ya saba wa Sunnah, ba ya kamata a yi shi)).

Sannan ya sake cewa cikin
wannan littafi nasa 29/239:-

(( ﻫﺬﺍ ﻣﻜﺮﻭﻩ، ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﺿﻤﻬﻤﺎ ﻭﺟﻌﻠﻬﻤﺎ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺼﺪﺭ، ﻭﺟﻌﻞ ﺍﻟﻴﻤﻨﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻴﺴﺮﻯ ﻭﺍﻟﺮﺳﻎ ﻭﺍﻟﺴﺎﻋﺪ؛ ﻻﻧﻪ ﻗﺪ ﺛﺒﺖ ﻋﻦ ﺍﻟﻨﺒﻲ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﻣﻦ ﺣﺪﻳﺚ ﺳﻬﻞ ﺑﻦ ﺳﻌﺪ، ﻭﻭﺍﺋﻞ ﺑﻦ ﺣﺠﺮ،
ﻭﻫﻠﺐ ﺍﻟﻄﺎﺋﻲ ﻣﺎ ﻳﺪﻝ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ. ﺍﻣﺎ ﺍﻹﺭﺳﺎﻝ ﻓﻼ ﺩﻟﻴﻞ ﻋﻠﻴﻪ، ﺑﻞ ﻫﻮ ﺧﻼﻑ ﺍﻟﺴﻨﺔ)).

Ma’ana: ((Wannan makruhi ne, abin da yake Sunnah: Taro su da sanya su a kan kirji, da kuma sanya dama a kan tafin hagu da wuyan hannu, da dantse, saboda
ya tabbata daga Annabi mai tsira da amincin Allah daga hadithin Sahl Dan Sa’ad, da Waa’il Dan Hujur, da Hulb Attaa’ii abin da yake nuna hakan.

Amma sake hannaye
babu wani dalil a kansa, kai a
gaskiya ma shi sabanin Sunnah ne)).

(5) Idan wani ya ce: Ko a cikin
shugabannin Mazhabar Imam Malik akwai wadanda ke ganin cewa da zarar an samu wata fatawa a cikin Mazhabar malikiyyah wacce ta saba wa sahihiyar sunnar Manzon Allah, to, a yi watsi da ita, a koma a yi riko da sahihiyar sunnar Manzon Allah mai tsira da amincin Allah kawai?

Amsa a nan ita ce: Lalle akwai su da yawa, a gaskiya ma ni babu wani shahararre daga cikinsu da na sani yake cewa: Bayan Bamalike ya fahimci cewa sahihiyar Sunnah ta saba wa malikancinsa ya yi watsi da
sahihiyar Sunnar ya cigaba da yin aiki da abin da ya zo cikin mazhabarsa kawai!! Ni ban san wani mash’huri da ya fidi irin wannan magana mara kan gado ba.

Gaskiyan lamari shi ne: Abin
da shugabannin mazhaba suke cewa shi ne: Duk lokacin da wani kaulin mazhaba ya yi karo da
sahihiyar Sunnah to sai a jingine mazhabar a yi aiki da sahihiyar Sunnah.

Imam Malik da kansa
yana cewa kamar yadda ya zo cikin littafin Tartiibul Madaarik
1/182:-

(( ﺍﻧﻤﺎ ﺍﻧﺎ ﺑﺸﺮ ﺃﺧﻄﺊ ﻭﺃﺻﻴﺐ، ﻓﺎﻧﻈﺮﻭﺍ ﻓﻲ ﺭﺃﻳﻲ ﻓﻜﻞ ﻣﺎ ﻭﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺨﺬﻭﻩ، ﻭﻛﻞ ﻣﺎ ﻟﻢ
ﻳﻮﺍﻓﻖ ﺍﻟﻜﺘﺎﺏ ﻭﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﺎﺗﺮﻛﻮﻩ )).

Ma’ana: ((Ni ba kowa ba ne face mutum, ina yin kure kuma ina yin daidai, sai ku rika yin nazari cikin
ijtihadina, dukkan abin da ya dace da Alkur’ani da Sunnah sai ku rike shi, kuma dukkan abin da bai dace da Alkur’ani da Sunnah ba sai ku
bar shi)).

Sannan babban malami Jamaalud Dinil Qaasimii ya ce cikin littafinsa: Attahdiithu Fi Fununi Mustalahil Hadith shafi na 245, da babban malami Saalih Bin Muhammad Alfullaanii cikin littafinsa: Iiqaazu Himami Ulil Absar shafi na 89:

dukkansu biyun sun ce: Babban malami cikin mazhabar Malikiyyah
Muhammad Almaqqarii ya ce cikin littafinsa na Qwa’idul Fiqhi:-

(( ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﺗﺒﺎﻉ ﻇﺎﻫﺮ ﻧﺺ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﻣﻊ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻪ ﻷﺻﻮﻝ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ﻋﻨﺪ ﺣﺬﺍﻕ ﺍﻟﺸﻴﻮﺥ. ﻗﺎﻝ ﺍﻟﺒﺎﺟﻲ : ﻻ ﺍﻋﻠﻢ ﻗﻮﻻ ﺍﺷﺪ ﺧﻼﻓﺎ ﻋﻠﻰ ﻣﺎﻟﻚ ﻣﻦ ﺍﻫﻞ ﺍﻻﻧﺪﻟﺲ؛ ﻻﻥ ﻣﺎﻟﻜﺎ ﻻ ﻳﺠﻴﺰ ﺗﻘﻠﻴﺪ ﺍﻟﺮﻭﺍﺓ ﻋﻨﻪ ﻋﻨﺪ ﻣﺨﺎﻟﻔﺘﻬﻢ ﺍﻷﺻﻮﻝ ﻭﻫﻢ ﻻ ﻳﻌﺘﻤﺪﻭﻥ ﻋﻠﻰ ﺫﻟﻚ.

ﺍﻧﺘﻬﻰ. ﻭﻗﺎﻝ ﺃﻳﻀﺎ: ﻗﺎﻋﺪﺓ: ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺭﺩ ﺍﻷﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﻰ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻋﻠﻰ ﻭﺟﻪ ﻳﻨﻘﺺ ﻣﻦ ﺑﻬﺠﺘﻬﺎ ﻭﻳﺬﻫﺐ
ﺑﺎﻟﺜﻘﺔ ﺑﻈﺎﻫﺮﻫﺎ؛ ﻓﺎﻥ ﺫﻟﻚ ﻓﺴﺎﺩ ﻟﻬﺎ ﻭﺣﻂ ﻣﻦ ﻣﻨﺰﻟﺘﻨﺎ، ﻻ ﺍﺻﻠﺢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻤﺬﻫﺐ ﻟﻔﺴﺎﺩﻫﺎ، ﻭﻻ ﺭﻓﻌﻬﺎ
ﺑﺨﻔﺾ ﺩﺭﺟﺎﺗﻬﺎ، ﻓﻜﻞ ﻛﻼﻡ ﻳﺆﺧﺬ ﻣﻨﻪ ﻭﻳﺮﺩ ﺍﻻ ﻣﺎﺻﺢ ﻟﻨﺎ ﻋﻦ ﻣﺤﻤﺪ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ، ﺑﻞ ﻻ ﻳﺠﻮﺯ ﺍﻟﺮﺩ ﻣﻄﻠﻘﺎ؛ ﻻﻥ ﺍﻟﻮﺍﺟﺐ ﺍﻥ ﺗﺮﺩ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ
ﺍﻟﻴﻬﺎ )).

Ma’ana: ((Bai halatta bin zahirin nassin Imami tare da sabawarsa ga jigogin Shari’ah (Qur’ani da Hadithi) a wurin korarrun Shaihunai.

(Imam) Baajii ya ce:
Ban san wani kauli da ya fi
tsananin saba wa Malik ba kamar(kaulin) mutanen Andulus ba, saboda Malik ba ya halattar da bin masu ruwaya daga gare shi ba a
lokacin da suka saba wa Jigogi, su ba sa dogara a kan haka. Intaha.

Sannan (Imam Baajii) ya sake cewa: Qaa’idah: Bai halatta a yi raddin Hadithai zuwa ga mazhaba ta fiskar da zai rage wani abu na
armashinsu, kuma ya tafiyar da amincewa da zahirinsu, domin hakan bata su ne da kuma wulakanta matsayinsu. Kada Allah Ya kyautata mazhabobi ta hanyar
bacinsu (watau su hadithan) kada. (Allah Ya daukaka mazhabobin) ta hanyar karya darajarsu (su hadithan).

Dukkan wata magana
Ana iya aiki da ita, ana kuma iya yin watsi da ita, amma banda abin da ya inganta a wurinmu daga Muhammad mai tsira da amincin
Allah, ko kadan bai halatta a yi raddin (maganarsa), domin abin da ke wajibi shi ne: Yin raddin mazhabobi zuwa gare ta)) (watau maganar Annabi mai tsira da amincin Allah).

(6) Idan wani ya ce: Dalilan nan duka da ka kawo na cewa: dora dama a kan hagu cikin salla shi ne Sunnah, sake hannaye kuwa sabanin Sunnah ne, wasu mutane
za su ce ba su gamsu da su ba, hasali ma za su ce dukkan hadithan masu rauni ne, saboda haka yin salla hannaye a sake shi ne daidai domin shi ne abin da suka sani a mazhabar Malikiyya!!!
To, sai a ce da shi:

Na farko dai da
ma ba dukkan gaskiyar da masu wa’azi ke fada ba ne mutane ke karba, Annabawa da Manzanni sun gaya wa jama’arsu gaskiya, amma an samu mutane da yawa
wadanda suka karyata su, suka yi watsi da gaskiyar da suka fada musu. Wannan shi ya sa za ka ga ‘yan bidi’ah da yawa suna karyata ingantattun hadithan Buhari da Muslim suka ruwaito cikin
sahihansu, matukar dai hadithan sun saba wa abin da Dagutansu suka dora su a kan shi iyazan billah!

A bu na biyu shi ne: Ciwon son zuciya na da wahalar waraka, wannan shi ya sa duk yadda masu wa’azi suka yi kokarin fahimtar da Kiristoci cewa aqidarsu ta cewa Allah yana da Da watau Isa, kuma shi Allah Dayan uku ne! watau: shi ne Allah Uba, sannan kuma akwai
Allah Da! Sannan kuma akwai Allah Ruhu Mai tsarki!

Duk lokacin da masu wa’azi suka yi kokarin fahimtar da su cewa wannan kure ne bayyananne sai ka ga cewa
suna ta kawo tawilce-tawilce da wasu shubuhohi domin tabbatar da ra’ayinsu marar makama da hujja!!

Haka nan in ka dubi yan bidi’ah nau’i daban-daban da ake da su cikin Al’ummar Musulmi za ka rika ganin yadda suke zaburowa da
karfi suna kare son zuciyarsu.

Misali yanzu in ka yi kokarin
fahimtar da batijjane cewa:
aqidarsa ta cewa Salatul Fatihi saudaya tana daidai da Alkur’ani sau dari shida wanda wannan yana nufin ke nan Salatul Fatihi ta fi Alkur’ani sau dari biyar da casa’in da tara!! In ka shaida musu cewa wannan akidah tasu wani nau’i ne na ilhadi da raina Littafin Allah
Madaukakin Sarki, to nan da nan za ka ga cewa sun yi ca a kanka da zage-zage, da bace-bace, kuma za ka ga cewa sun nace suna ta
yin tawilce-tawilce domin su
tabbatar da son zuciyarsa!!
To amma irin wannan hayaniya ta yan bidi’ah, da ‘yan bin son zuciya sam bai kamata ba a ce za ta hana
masu wa’azi ci gaba da shiryar da Al’ummah zuwa ga sahihiyar sunnar Annabi mai tsira da amincin Allah ba.


Muna rokon Allah muna kaskantar da kai a gabanSa da ya tausaya Ya nuna mana gaskiya gaskiya ce Ya ba mu ikon bin ta, Ya kuma nuna mana karya karya ce Ya ba
mu ikon guje mata. Ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *