1. Babu ingantaccen Nassi daga Annabi mai tsira da amincin Allah koda daya ne a kan yin Sadlu cikin salla, amma ingantattun hadithai da yawa ne daga shi Annabi mai tsira da amincin Allah da suka yi nassi a kan yin Qabdhu cikin salla, wannan shi ne ma ya sa rinjayen Ahlus Sunnah Wal Jama’ah suka bi sunnar Manzon Allah suke yin sallarsu tare da dora hannayensu na dama a kan na hagu.

2. Amma manyan kungiyoyin ‘Yan bidi’ah na duniya, kamar su: Shi’ah, da Ibaadhiyyah (Khawaarijawa) su wadannan ba sa dora dama a kan hagu cikin sallolinsu, a’a suna yin salla ne hannayensu a sake.

3. Su ma mabiya mazhabar Malikiyyah da yawa daga cikinsu suna yin salla ne hannayensu a sake, tamkar yadda Shi’ah da Khawaarij suke yi, duk da yake almajiran Imam Malik na Madina su kam Qabdhu suke yi ba Sadlu ba, kamar yadda Ibnu Abdul Barri ya ce cikin Alis Tizkar 2/291, da At-Tamheed 20/75.
Babban Malami Salihul Fulaaniy ya ce cikin littafinsa Iqaazul Himam shafi na 98

((وقد لهج المتاخرون من المالكية بترجيح القول والرواية بمجرد وجودها في المدونة ولو خالف الكتاب والسنة الصحيحة السالمة من المعارضة والنسخ وتركوها لاجل رواية ابن القاسم في المدونة عن مالك مع ان رواية القبض ثابتة عن مالك واصحابه بروايات الثقات من اصحابه وغيرهم)).

Ma’ana: ((Hakika Maluman karshe- karshe na Malikiyyah sun hurta rinjayar da Kauli da Riwayah saboda samuwarsu kawai cikin Mudawwanah koda kuwa ya saba wa Alkur’ani da ingantacciyar Sunnah wacce ta kubuta daga wata kalu-bala ko naskhi, suka bar ta (watau ingantacciyar Sunnar) saboda riwayar Ibnul Qasim cikin Mudawwanah daga Malik, duk da yake riwayar Qabdhu tabbatacciya ce daga Malik da sahabbansa ta hanyar riwayoyin Amintattu daga sahabbansa da wasunsu)).

4. Idan wani ya ce: Ai an ce Sahabi Abdullahi Bin Zubair, da Tabi’i Al-Hasanul Basariy, da Tabi’i Ibrahimun Nakha’iy dukkan wadannan an ce sadlu suke yi a cikin sallarsu; saboda haka me zai hana ni ni ma in bar yin aiki da abin da Annabin ya ce in koma in yi aiki irin na wadannan Magabatan?
Sai a ce da shi: dukkan wadannan da ka ambata mutane ne masu daraja kuma abin girmamawa ga dukkan Musulmin kwarai, to amma su ba ma’asumai ba ne, a’a suna iya yin kure suna kuma iya yin daidai cikin ayyukansu na addini. Sannan cikinsu din nan dukkansu babu wanda ya san dukkan hadithan Annabi mai tsira da amincin; saboda haka ta yiwu sun yi sadlu ne saboda ilminsu bai kai ga sanin hadithan Qabdhu ba, ta yiwu kuma ba su yi qabdhun ba ne saboda wani uzuri daban. To amma dai koma mene ne ya sa suka yi abin da suka yin kai a matsayinka na wanda hadithan Annabi suka inganta a gabanka a kan wata mas’ala to dole ne ka bi abin da Annabi ya ce ka kuma bar abin da ya saba wa abin da shi ya fadan matukar dai Allah kake son bautawa ba Shaidan da son zuciyarka ba. Wannan shi ne Shari’ah rashin yin haka fadawa ce cikin bidi’ah da bata da halaka. Muna rokon Allah Ya taimake mu.

105 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *