A iya sanina ni Kungiyar Hamas Ahlus Sunnah ne ba Shi’ah ba; wannan shi ne ma ya sa idan shugabanninsu za su fara yin jawabi su kan fara ne da yi wa Annabi da alayensa da sahabbansa salati da taslimi, ga kuma al’ada masu akidar Shi’a ba sa yi wa Sahabbai salati da taslimi.

Tabbas gwamnatin Shi’a ta Iran tana goyon bayan Hamas wannan kuma abin a yaba ne, haka nan kuma tabbas gwamnatin Sunnah ta Turkiyya ita ma tana taimakon Hamas. Wannan kuma ba su kadai ba ne suke taimakon su, a’a da yawa daga cikin gwamnatocin kasashen Larabawa wadanda ‘yan Sunnah ne suke jagorancinsu su ma suna taimakon Hamas sosai.

Ke nan kure ne babba wani ya fito fili ya gaya wa Duniya cewa Hamas ‘yan Shi’a ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *