1. Yana daga cikin biyayya ga Annabi mai tsira da amincin Allah nuna yarda da cewa dukkan bidi’ah bata ce har abada.
  2. Lalle kure ne babba wani ya kiyasta bidi’ah a kan hukunce-hukuncen taklifin nan guda bayar, watau ya rika cewa: akwai wata bidi’ah wajiba, ko wata bidi’ah muharrama, ko wata bidi’ah mustahabba, ko wata bidi’ah makruha, ko wata bidi’ah mubaha!!
  3. Tabbas ba a taru aka zama daya ba, a cikin Sufaye ma akwai wadanda suka fadi daidai a cikin wannan babin, cikinsu kuwa akwai Sheikh Ibrahim Nyass a inda ya ce a cikin littafinsa: Tabsiratul Anaam Fii Annal Ilma huwal Imam shafi na 58:-
    ((والحق ان لفظة “الكل” في هذا الحديث وفي كل حديث ورد بمعناه على حقيقتها، وقسمة البدعة الى الاقسام المذكورة والى الحسنة والسيئة ليس عليها اثارة من علم؛ لانه لم يرد دليل دال عليها ولم يرد حديث في هذا الباب، ولا رائحة القسمة قط، والامثلةالمشار اليها ليست من البدع على الاطلاق…)).
    Ma’ana: ((Abin da yake gaskiya shi ne: lafazin “Al-Kullu” cikin wannan hadithin da ma cikin dukkan wani hadithi da ya zo da ma’anarsa yana nan a bisa ma’anarsa ta hakika, raba bidi’ah zuwa ga kashe-kashen da aka ambata, da zuwa bidi’ah kyakkyawa da mummuna babu wani burbudin ilmi a kansa; domin babu wani dalili da ya zo da haka, babu kuma wani hadithi da ya zo cikin wannan babin, kuma da dai babu wani kanshin daidaita cikin hakan. Sannan misalan da aka yi ishara zuwa garesu a yanke ba sa daga cikin bidi’o’i…)).
  4. Allah muke roko har kullum da Ya taimaki al’ummarmu ta yadda za su rika girmama maganar AnnabinSa mai tsira da amincin Allah, kuma su rika yin biyayya ga hukuncin da maganar ke dauke da shi. Ameen.

108 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *