“Dr. Ibrahim Jalo Jalingo kabar zagin yan darika kayi izala su kuma suyi darika sai za6e yazo kace muhada kai tayaya Aminu Zakari“
Dan’uwa a ina ne zagin ‘yan darika da Dr. Jalo yake yi?
Ni ina ganin cewa idan har kai ba ka san wane ne Dr. Jalo ba ai su ‘yan darika sun san ko wane ne shi, kuma ba sa bukatar irinka ko irin mai kama da kai ya sanar da su wane ne shi Dr. Jalo a jihar Taraba, ko wane ne Dr. Jalo a Nigeria. Gaskiyan al’amari shi ne hatta su azzalumai daga cikin kiristoci wadanda kai kake bauta wa su ma sam ba sa bukatar ka koya musu wane ne Dr. Jalo a jihar Taraba, ballantana suka maka wata biya a kan wannan sabuwar hidimar da ka yi musu.
Yana da kyau ka san cewa ‘yan darika musulmi ne ko da kuwa suna yin bidi’ah da yawa; saboda haka irin yadda kake jin Dr. Jalo yake son Musulunci ya kamata ka san cewa su ma haka suke son Musuluncin, dukkan wata kuntatawa da wasu daga cikin kiristoci ke yi wa musulmi a jihar Taraba su ma wannan kuntatawar ta shafe su ciki da waje.
A ganina irinka irinka masu bautar maslahar kansu ba su isa su raba ‘yan darika da jin zafin irin yadda ake share al’ummar musulmin jihar Taraba ba ta hanyar karantar da su cewa Dr. Jalo member ne a kungiyar Izalah, ba kuma member ba ne a cikin daya daga cikin kungiyoyin darika ba. Yana da kyau ka san haka.
Gwagwarmayar nema wa al’ummar musulmin jihar Taraba ‘yancin siyasa da hakin shugabantar jihar Taraba a matsayinsu na masu rinjaye a cikin Jihar da Dr. Jalo yake yi sam ba alfurma ba ce yake yi wa ‘yan darika, a’a, yana sauke wajibcin mutuntaka da addini ne da yake a kansa kawai. Haka su ma kuma ‘yan darika gwagwarmayar da suke yi domin nema wa al’ummar musulmi ‘yanci a jihar Taraba ba don Dr. Jalo ba ne suke yin ta, a’a suna yi ne domin sauke wajibicin mutuntaka da addini ne da yake kansu, saboda haka ni a ganina ban ga ta inda ireirenka bayin maslahar kansu za su shigo su hana wadannan bangarori biyu aikin addini da mutuntaka da suke yi wa kansu da al’ummarsu ba.
Ina ganin cewa lalle tun ranar da aka san Dr. Jalo ne, ake kuma sanin cewa tabbas shi din nan tun a ranar ne yake member cikin kungiyar Izalah, kuma yake yi wa mutane wa’azin cewa su daina idin mauludi, yake kuma yin musu wa’azin cewa wajibi ne ko wane musulumi ya yi musuluncinsa kamar yadda yake rubuce cikin Alkurani da Hadithi, saboda haka wannan shirmen da ka rubuta wa Duniya mene ne zai kare ka da shi a idanun azzaluman kiristicin da kake tsugunawa a gabansu domin su ba ka??
Tabbas da ‘yan darika da kuma su iyayen gidanka azzalymai daga cikin kiristoci ko wanne daga cikinsu wannan shirme naka ba zai kare su da kome ba; domin sun fi ka sanin wane ne Dr. Jalo a Taraba.